(ABNA24.com) Gwamnatin kasar Iran ta bada sanarwan cewa ta gano hanyoyin Tunkarar tasirin da takunkuman tattalin arzikin da kasar Amurka ta dorawa kasar suke yi a kan tattalin arzikin kasar, don haka takurawan da gwamnatin Amurka takewa kasar ba zai sami nasara ba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Abbas Musawi yana fadar haka a safiyar yau Asabar, ya kuma kara da cewa, sabbin takunkuman da Amurka ta dorawa babban bankin kasar a jiya ba sabon abu bane, takunkumai wadanda ta dorawa bankin a baya.
Musawi ya kara da cewa yakamata gwamnatin kasar Amurka ta san cewa wuce gona da iri wajen amfani da takunkuman tattalin arziki kan kasar Iran ba zai kara wani tasiri a kan tattalin arzikin kasar ba. Sannan ya ce wannan halin ya maida Amurka saniyar ware a harkokin tattalin arziki a bangarori da dama a duniya.
Daga karshe Musawi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran ta riga ta gano hanyoyin magance tasirin takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dorawa kasar daga cikin gida, da kuma aiki da kawayenta na kasashen waje.
A jiya jumma’a ce dai ma’aikatar kudi ta kasar Amurka ta bada sanarwar kara kakabawa babban bankin kasar Iran da wasu cibiyoyin kudade a kasar takunkman tattalin arziki.
/129
22 Satumba 2019 - 04:46
Lambar labari: 977085
Gwamnatin kasar Iran ta bada sanarwan cewa ta gano hanyoyin Tunkarar tasirin da takunkuman tattalin arzikin da kasar Amurka ta dorawa kasar suke yi a kan tattalin arzikin kasar, don haka takurawan da gwamnatin Amurka takewa kasar ba zai sami nasara ba.